Ana neman mafita kan rikicin Sudan
January 23, 2025
Dakarun RSF na ragargazar garin Fasher na yankin Arewacin Darfur bayan karewar wa'adin kwanaki biyu da suka bai wa mazaunansa da ko dai su mika wuya, domin su shiga birnin da ya gagaresu duk da yunkurin shigarsa har sau fiye da 80, ba tare da sun yi nasara ba, sakamakon turjiyar da mazaunansa da suka dauki makamai ke nunawa, ko su fuskanci mutuwa.
Tuni dai Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Right a Sudan, ta bakin kakakinta ta soki bangarori masu yakin da jefa mazauna yankin na Fasher cikin hatsarin ba gaira ba dalili.
Karin Bayani: Sojojin Sudan na samun nasara kan 'yan tawayen RSF
Wannan gagarimin farmakin kan birnin na Fasher dai na zuwa ne mako guda bayan da rundunar yan tawayen ta RSF ta tafka mummunan asarar,bayan da rundunar sojin gwamnati ta kwace iko da birnin Madani mai matukar mahimmanci a bangaren soji da tattalin arziki, lamarin da ya sanya masharhanta ke cewa rundunar ta RSF na kokarin farfadowa ne daga mummunar asarar da ta karya gwiwar sojojinta.
A daura da haka, bangarrorin siyasar kasar ta Sudan mabanbanta na taro a birnin Nairobi na Kenya, kan yadda za su kafa gwamnatin hadin kan kasa ta fararen hula zalla da za ta nemi halarci daga kasashen duniya, don maye gurbin gwamnatin sojin da Janar Abdel Fattah Burhan ke jagoranta daga birnin Port Sudan, shirin da akai ammanar yana da matukar wuya da sarkakiya a iyar aiwatar da shi a lokacin da rugugin bindigogi ke kara kaurewa a kasar.
Duk hakan dai na karawa fararen hula da 'yan gudun hijirar kasar ta Sudan a cikin gida da ma ketare, tarin takaici.
A lal misali a kasar Libiya, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta yi tir da yadda ake bautar da daruruwan 'yan gudun hijirar kasar ta Sudan da cin zarafinsu gami da yi wa matansu da ke sansanonin 'yan gudun hijira fyade barkatai ba tare da sun samu kariya daga jami'an tsaron da ake zargin wasusnsu da hannu wajen tafka aika-aikar.