Kasashen yankin gabashin Afirka na kokarin ganin sun kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu da ya kwashe tsahon makwannin uku, wanda kuma ya haddasa asarar rayuka da dama.
Talla
Bangarorin dake gaba da juna a Sudan ta Kudu na shirin fara tattaunawar sulhu a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, a wani sabon mataki na kawo karshen yakin da suke gwabzawa a tsakaninsu.