1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin nakasa tattalin arzikin Kamaru

Binta Aliyu Zurmi
March 7, 2019

'Yan awaren kasar Kamaru masu amfani da harshen Ingilishi sun sha alwashin kaurace wa kayayyakin gwamnati kamar su barasa da ke fitowa daga yankin da ke amfani da harshen Faransanci.

Kamerun Straßenverkehr in Yaounde
Hoto: picture-alliance/dpa

Barasar kasar ta Kamaru da ta shahara ita ce "33 export" ta kamfanin Brasserie, tuni kuma wannan barasa ta fara bacewa a shaguna da mashaya da ke yankin 'yan awaren. Bacewar manyan barasa a yankin ya bar mutane da suka saba da ita da rashin zabi face su sha abin da ya samu. Polycarp da Simon sun saba da shan waccan barasa da aka hana shigar da ita yankinsu sun ce yanzu ba su da zabi illa su sha abin da suka samu.

Mercy na da shago siyar da barasa a garin na Nkwen ta bayyana yadda yanzu ta gaza samun sauran kalolin barasa daga kamfanin Brasserie, sai daga kamfanin Guinness kawai:

Mashaya barasar na da karancin zabiHoto: DW/K. Welter Beer

"Mun lura manyan motoci da ke safarar kayan kamfanin Brasserie sun dakata da zuwa, da muka tambaye su sai suka ce mayakan Ambazonia ne suka hana su kawowa.  Hatta masu siyar da kadan-kadan ma a cikin unguwa sun daina, wani lokaci ma ko mun samu mun siya a boye ba mai siya, wata rana ma mayakan sun zo sun mana kashedi inda suka ce kayan kamfanin Guinness da UCb kawai za mu siyar."

Kaurace wa kayayyakin barasa da yankin 'yan ambazonia ke yi na yin tasiri a yankin. 'Yan awaren na ganin hakan ne kawai zai sa su durkusar da tattalin arzikin kasar da kuma ake yakar su da shi.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani