1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sasanta rikicin Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 2, 2016

Sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry ya bude taro kan sasanta rikicin kasar Siriya a birnin Geneva.

Sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry tare da jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura
Hoto: Reuters/D.Balibouse

Taron dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fama da wani dauki ba dadi a birnin Aleppo na kasar ta Siriya. A yayin wata ganawa da ya yi da takwaransa na kasar Saudiya Adel al-Jubeir da kuma babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura, Kerry ya ce suna ci gaba da tattaunawa kullum domin ganin an samar da mafita, kuma yana ganin akwai haske:

"Muna daf da kai wa ga fahimtar juna, sai dai muna da jan aiki a gabanmu, shi ne dalilin da ya sa muka sake hallara a nan."


Kerry ya kara da cewa a yanzu haka suna yin iya kokarinsu domin ganin an rage tashin hankalin da ake tsaka da fuskanta a birnin na Aleppo.