1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shigar da agajin gaggawa a Siriya

Abdoulaye Mamane Amadou
February 13, 2023

Kwamtin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin wata ganawar sirri a wannan Litinin game da batun kai agajin jinkai a yankin da iftila'in girgizar kasa ta daidaita a Siriya.

Für Artikel: DW Middle East - Assad nutzt Erdbeben politisch aus
Hoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths da ya kai ziyara a karshen makon jiya a kasashen Turkiyya da Siriya, zai gabatar da cikakken rahoton halin da ake ciki game da bukatar kai kayan agaji a kasashen biyu.

Tun da farko ma dai sai da shugaban hukumar ya bayyana kasawar kasashen duniya game da shigar kayyakin agaji musamman a yankin arewa maso yammacin Siriya, kazalika shugaban ya bayyana cewar da akwai bukatar bude hanyoyin shigar da kayayakin agaji ga mabukata a cikin hanzari.

Ya zuwa yanzu dai iftila'in girgizar kasa a kasashen Turkiyya da Siriya ya halaka akalla mutane fiye da dubu 35, baya ga wasu dubban jama'ar da suka jikkata.