Yunkurin ta'addanci ya ci tira a Beljiyam
March 23, 2017Talla
Jami'an tsaro a kasar Beljiyam a ranar Alhamis din nan sun yi nasara ta cafke wani mutum da ya yi kokari na kutsa kai cikin jama'a da suka fita rukunin shaguna dan yin cefane a birnin Antwerp, kamar yadda shugaban 'yan sanda a wannan birni ya bayyana.
A cewar shugaban 'yan sanda a wannan gari Serge Muyters mutumin da ya yi wannan yunkuri ya fito daga kasashe da ke a Arewacin Afirka.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda da kai hari ta hanyar amfani da mota da wuka a Birtaniya abin da ya yi sanadi na rayukan mutane uku kuma kwana guda bayan cika shekara guda da harin birnin Brussels wanda ya yi sanadi na rayukan mutane 32.