Yunkurin takaita bada mafaka a Jamus
January 29, 2016Talla
A bara kadai kasar Jamus ta shigar da sunayen mutane miliyan daya da suka nemi a basu mafakar siyasa. Kuma yanzu gwamnati na fatan takaita wannan lamarin. Jagoran jam'iyar SPD Sigmar Gabriel, yace kasashen Moroko, Tunisiya da Aljeriya a sasu a matsayin kasashen da ake zaman lafiya, wadanda ma'ana 'yan kasar basa bukatar mafakar siyasa. Kuma yace a yarjejeniyar da suka cimma za'a dakatar da bada visar hadewar iyalai na shekaru biyu. Kudurin dai na bukatar sa hannun majalisar dokoki da ta zartaswa kan ya zama doka.