Yunkurin zaman lafiya a Kongo
December 1, 2012'Yan tawayen M23 da suka kwace iko da garin Goma na hamhuriyyar Doimokradiyyar Kongo tun a ranar 20 ga watan Nuwamban nan, sun fara janyewa daga garin suna yin wake-wake da wasa da makamai a wannan Asabar. Wannan matakin da suka dauka dai ya karfafa fatan kokarin samar da zaman lafiya da kuma tattaunawar kawo karshen rigingimun da yankin ya fada ciki a baya bayannan.
Kimanin mako guda kenan da shugaban Uganda, dake zama shugaban kungiyar kasashen yankin Great Lakes ya jagoranci wani shirin sulhu, wanda a lokacin ne kuma ya bukaci 'yan tawayen su janye daga birnin na Goma bayan da suka fatattaki sojojin gwamnatin jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. A da dai 'yan tawayen sun sha alwashin kifar da gwamnatin shugaba Josef Kabila, wadda ke da hadikwata a birnin Kinshasa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou