1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Yunus ya yi rantsuwar kama aiki a kasar Bangladesh

August 8, 2024

Muhammad Yunus da ya lashe kyautar Nobel ya koma Bangladesh don jagorantar gwamnatin rikon kwarya bayan da aka kawo karshen mulkin Sheikh Hasina. Sai dai akwai kalubale a gabansa na maido da kasar cikin hayyacinta.

Muhammad Yunus ya fara shugabantar gwamnatin rikon kwarya a Bangladesh
Muhammad Yunus ya fara shugabantar gwamnatin rikon kwarya a BangladeshHoto: MUNIR UZ ZAMAN/AFP

A kwarya-kwaryar jawabin da ya gabatar bayan rantsuwar kama mulkin Bangladesh Muhammad Yunus ya ce kasar ta samu ‘yanci na biyu a hukumance bayan gwagwarmayar da magabatan farko suka yi. A don haka ya ce akwai bukatar tattabar da wannan ‘yanci da jajircewa wajen ciyar da kasar gaba.

Muhammad Yunus ya kasance mutum daya tilo da dalibai da daukacin al’ummar kasar suka yi amannar cewa zai gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci da rikon amana, duk da cewa akwai tarin kalubalen da ke gaban Yunus kama daga tabbatar da tsaro da kuma bin doka da oda a fadin kasar tare da mayar da dalibai makarantu har ma da mayar da miliyoyin al;ummar kasar gidajensu.

Matasa na nuna wa Muhammad Yunus goyon baya a DhakaHoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS

Wasu mazauna birnin Dhaka sun ce suna da burin garin Bangladesh da kowa yake fata, kamar yadda Abu Sayed ke cewa: " Babban burin daukacin matasan kasarmu na kawo sauyi shi ne sake gina kasa, muna fatan shugaba Yunus zai tabbatar da wannan buri na gina kasarmu” 

Karin bayani: EU ta bukaci a kwantar da hankali a Bangladesh

Parvez Sheikh wani matashi ne da ke zaune a birnin Dhaka, ya bukaci jan layi kan dukkan nin al amuran da suka faru a baya, inda ya ce" Muna bukatar zaman lafiya mai dorewa a  Bangladesh din da za a wayi gari babu zancen jam‘iyyar Awami League ko BNP ko kuma sauran jam’iyyun da ke da ra’ayin haifar da tazgaro a dimukradiyya. Ina son na manta dukkan abubuwan da suka faru a baya domin na ci gaba da rayuwa mai inganci."

Ana sa ran Muhammad Yunus zai taka rawar gani a BangladeshHoto: Raphael Lafargue/abaca/picture alliance

An bayar da rahotanni ci gaba da kamen jami'an jam'iyyar Bangladesh ta "Awami League" da ke zama jam'iyyar tsohuwar Firaiminista Sheikh Hasina, wacce aka hambarar daga mulki. Sai dai jam'iyyar ta ce a shirye take ta tattauna da 'yan adawa da kuma sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta Muhammad Yusus. Mukarraban tsohuwar firaminista da a baya suka ce za su kauce wa shiga siyasa suka ce ya zama wajibi su shiga a dama da su, in ji dan Hasina mai suna Sajeeb Wazed Joy.

Karin haske: Bangaladash: Firaminista Hasina ta yi murabus

Wazed Joy Ya ce: "Na ce iyalan gidanmu mun ce ba za su sake shiga harkokin siyasa ba, amma yadda ake kai wa shugabannin jam'iyyarmu da ma'aikatanmu hari, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, ba za mu nade hannuwan ba”

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani