1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin cimaka ta mamaye kasashen Afirka

Abdoulaye Mamane Amadou
December 3, 2020

Mutane fiye da miliyan 16 ne ke fama da karancin abinci a cikin wasu kasashe 15 na yankin Sahel da yammacin Afirka a cewar hadin gwiwar kungiyoyin yaki da karancin cimaka na (RPCA).

Nigeria Maßnahmen gegen die Wüstenbildung
Hoto: DW/Thomas Mösch

Kungiyoyin na zargin tashe-tashen hankula masu nasaba da rashin tsaro a kasashen musamman ma a yankin Arewacin Najeriya a matsayin kan gaba wajen hadasa karancin abincin, kana kuma muddin ba a dauki matakan da suka dace ba a gabanin karshen damanar badi, mutane akalla miliyan 24 ka iya fadawa cikin mummunar yunwa a yammacin na Afirka daga watan Yuni zuwa watan Agustan 2021.

Kasashen Najeriya da Burkina Faso ne ke kasancewa cikin tsananin yuwa a cewar kungiyoyin, sakamakon tsanantar da ake fuskanta na hare-haren 'yan bindiga da masu da'awar jihadi a cikin kasashen.