Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya fara amfani da jiragen sama, wajen samar da agajin gaggawa ga dubban iyalai a jihar Upper Nile ta kasar Sudan ta Kudu.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya na kai agaji ta sama a Sudan ta Kudu Hoto: Florence Mettiaux/AP/picture alliance
Talla
Wannan rabon ya kasance na farko cikin sama da watanni hudu ga mutane sama da dubu 40 da ke fuskantar kangin yunwa a sassan kasar ta Sudan ta Kudu. Fiye da mutane miliyan daya a fadin jihar Upper Nile na fuskantar matsananciyar 'yunwa, ciki har da mutane sama da dubu 32 da suka riga suka fuskanci mataki mafi girma na karancin abinci. Wannan adadi ya ninka sau uku tun bayan barkewar rikici a watan Maris. Hakan ya haifar da hijirar mutane musamman ma a kan iyakar Sudan ta Kudu da Habasha, inda shirin na WFP ke bayar da agajin abinci ga mutane kusan dubu 50 da suka tsere daga jihar ta Upper Nile domin tsaira da rayukansu.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar WFP, na da niyyar samar da abinci ga mutane dubu 470 a Upper Nile da Arewacin Jonglei a lokacin da ake fama da kamfar abinci. Amma ci gaba da fada da matsalolin jigilar kayan aiki suna hana magance kalubalen da ake fuskanta, duk da son isar da ton 1,500 na abinci ta ruwa. Nyaguar Tor da ke neman mafaka daga Sudan ta Kudu, ta ce rikicin da ake fama da shi a kasarsu ne ya hanasu su yin noma.
Mundari: Kabilar da ta yi nisa da rikicin Sudan ta Kudu
'Yan kabilar Mundari na zaune a wani yanki da ke da nisan tafiyar sa'o'i hudu daga Juba babban birnin Sudan ta Kudu. Kiwon shanu shi ne abin da mutanen suka fi raja'a a kai. A lokacin sanyi su kan kauracewa yankin nasu.
Hoto: Eric Lafforgue
Wajen yin kiwo a lokacin sanyi
'Yan kabilar Mundari ke nan da shanunsu, inda suke yin kiwo a wani yanki da ba shi da tazara sosai da garin Terekeka. Mutanen kan zo nan ne domin nemawa shanunsu abinci. Dole ne shanun su ketara kogin Nilu domin isowa nan, wanda hakan kan tayar da hankalinsu saboda gudun yin asarar dabbobinsu.
Hoto: Eric Lafforgue
Muhimmancin shanu ga 'yan Mundari
A kowacce safiya, a kan shafawa shanun toka domin kawar da kwari da kaska da ka iya yi musu illa. Baya ga haka ana goge kahon don ya yi sheki. Shanu na da mutakar muhimmanci ga 'yan kabilar Mundari, domin idan mutum ba shi da su, ba zai iya aure ko kasuwanci ko kula da iyali da sama musu abinci ba.
Hoto: Eric Lafforgue
Alakar Mundari da Larabawa
A lokacin da suke hutawa, 'yan kabilar Mundari kan sha irin tabar nan ta Shisha, wanda hakan ke nuna rin alakarsu da Larabawa. A shekara ta 2011 ne kasar Sudan ta rabu gida biyu. 'Yan Mundari sun shafe tsawon lokaci suna rikici da Arewa da kan gujewa shari'ar Musulumci da gwamnatin Khartoum ke amfani da ita.
Hoto: Eric Lafforgue
Zane irin na gado
Irin zanen gado da 'yan Mundari kan yi a goshinsu na nuna cewar mutum ya kawo karfi. Ana kuma iya amfani da zanen wajen gane inda mutum ya fito, sannan matsafa kan ce zanen na nuni da hukuncin kisa da aka yankewa wani. Ana amfani ne da wuka wajen yin irin wannan zanen, amma kuma hakan na kara hadarin kamuwa da cutar HIV/AIDS ko kuma SIDA.
Hoto: Eric Lafforgue
Zaman lafiya ya haifar da tsadar aure
Yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Salva Kiir da abokan hamayyarsa suka amince da ita, na nufin za a janye sojoji daga yankuna da dama. Hakan ya sanya matasa da yawa sun shiga neman matan da za su aura. Hakan ya sa sadaki ya kara tsada, inda yanzu ake bayar da shanu 40 maimakon 20.
Hoto: Eric Lafforgue
Dawowar 'yan gudun hijira
Paul dan gudun hijira ne da ya koma kauyen, bayan da ya shafe shekaru tara a sansanin 'yan gudun hijira na Kukuma da ke kasar Kenya. Matashin na son komawa makaranta domin ci gaba da karatunsa, sai dai wata kungiyar farar hula na son ganin ya biya dala 50 a kowacce shekara. Wannan kudi ya yi wa mahaifinsa yawa matuka.
Hoto: Eric Lafforgue
Busa kaho wajen kiran shanu
Nan wani dan Mundari ne yake busa kaho domin kiran shanunsa. Karar busar yana kaiwa wurare masu nisa. Wannan abu kan kasance mai hadari, domin ya kan haifar da rikici tsakanin 'yan Mundari da 'yan kabilar Dinka. A lokuta da dama a kan kwashe shanunsu a kadasu babban birnin kasar domin sayar da su, kuma mutane masu dauke da manyan bindigogi ne kan yi hakan.
Hoto: Eric Lafforgue
Fata na samun sauyin rayuwa
Matasan Mundari na mafarkin samun rayuwa mai inganci nan gaba. Galibinsu sun san yadda sauran sassan duniya suke ne kawai, ta hanyar hotunan da suke gani a wayoyinsu na salula. Ga alama fatansu ya kusa tabbata, domin Chaina za ta gina wani titin mota da zai hade Juba da Terekeka, kuma tazarar ba za ta wuce tafiya ta sa'a guda ba.
Hoto: Eric Lafforgue
Hotuna 81 | 8
Karancin tallafin kudi daga kasashen duniya na kara ta'azzara mummunan halin jin-kai da ake ciki a Sudan ta Kudu, wannan gibin kudin ne ya sa WFP bayar da fifikon taimakon abinci ga mutane miliyan biyu da dubu 500 masu rauni wato kaso 30 cikin 100 na masu tsananin bukata. A halin yanzu Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar na bukatar dalar Amurka miliyan 274 cikin gaggawa, domin ci gaba da samar da abinci ga 'yan Sudan ta Kudu har zuwa watan Disamba. Tun a watan Maris na 2025 ne fada a jihar Upper Nile ta Sudan ta Kudu ya raba dubban mutane da muhallansu, tare da jefa wasu da dama cikin mawuyacin hali na yunwa a cewar Daraktar WFP a Sudan ta Kudu Mary-Ellen McGroarty.
WFP da abokan hulda na bayar da fifikon tallafin abinci na gaggawa ga 'yan Sudan ta Kudu da suka fi rauni musamman mata masu juna biyu da masu shayarwa da yara 'yan kasa da shekaru biyar, a cewar shugaban ofishin WFP na Gambella Kudzayi Mazumba. Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar WFP na bayar da Biscuits mai dauke da sinadarin gina jiki domin magance tamowa da yara 'yan kasa da shekaru biyar ke fama da ita a Sudan ta Kudu.