1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

‘Yan gudun hijirar Habasha na fama da yunwa

Andrew Wasike FD/ZU/MA
July 11, 2023

Dubban 'yan gudun hijirar Habasha na fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon dakatar da kai agajin abinci da kungiyoyi suka yi.

Hoto: Ashraf Shazly/AFP

A watan da ya gabata ne dai, hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da kai tallafin kai abinci zuwa kasar da ke zama ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka saboda zargin karkatar da abinci.

Sansanin 'yan gudun hijira na Qoloji na kasancewa sansani mafi girma a kasar Habasha da ke dauke da fiye da mutane dubu 100 kuma yana daga cikin sansanin da ke fama da rashin abinci. Yawancin 'yan gudun hijirar sun bar matsugunnasu ne sakamakon fadan da ya barke a yankin Tigray na kasar. Yanzu haka suna cikin hali na tsanannin bukatar dauki musamman ma ga iyalan da suka dogara kaco-kan kan tallafin abinci daga kungiyoyin agaji.

Daga daga cikin  ‘yan gudun hijirar mai suna Abeba wadda 'yar kasuwa ce kafin rikici ya rabata da matsugunnanta, ta ce dakatar da samun tallafin abincin tamkar an fama musu sabon miki ne. Wani dattiji mai sunaTesfaye mai shekaru 60 ba shi da masaniyar inda zai samu abun da zai sanya a baka ko ma ya ba 'ya'yanshi 17.

"Ina da mata biyu, guda na da yara bakwai yayin da dayar ke da 10, kenan mu 20 ne a gidanmu. Muna fuskantar fari kuma muna tsoron kar mutane su fara mutuwa saboda a kalla kowane mutum ya kamata ya ci abinci sau biyu a rana, idan ba mu samu abinci ba, cutar tamowa za ta kama mutane‘‘ in ji Tesfaye.

Tuni dai hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara aiki da gwamnatin Habasha domin dinke barakar da ta kunno kai na sace abinci da ma badakalar cin hanci da ta kunno kai wajen rabon abinci. Hukumar dai ta yi zargin a wasu lokutan ana karkatar da kayan abinci; ba su zuwa wurin mabukata yayin da a wasu lokutan kuma ake siyar da wasu a kasuwannin kasar