1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yunwa ta sa mutane sun koma cin ganye a Gaza

July 11, 2024

Tsananin yunwa ce ta sa mutanen na Gaza komawa ga ganye domin rashin kayan abinci sakamakon yaki da Isra'ila le ki da Hamas a zirin

Hoton wani yaro da ke jiran abinci a Gaza
Hoton wani yaro da ke jiran abinci a GazaHoto: Hatem Khaled/REUTERS

Al'umma a Gaza da ke fama da yaki sun fara tsinkar ganye suna ci saboda rashin abinci a yankunansu.

An fara yakin ne bayan da mayakan Hamas suka far wa Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban shekarar 2023 inda suka kashe mutane akalla 1200 da kuma garkuwa da sama da 250 kamar yadda kididdigar Isra'ila ta nuna.

WFP: Gaza na cikin halin yunwa

Bayan shafe watanni tara ana gwabzawa tsakanin Hamas da Isra'ila, ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa sama da dubu 38.

A Gaza dai akwai mutum miliyan 2.3 wuri da ake wa kallon daya daga cikin mafiya cinkoso a duniya.

 

A yanzu ana karancin dukkan ababen more rayuwa kamar su ruwa da wuta da abinci da magunguna a Gaza lamarin da ke kara jefa mutane cikin hadari.