1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Tijani LawalOctober 23, 2009

Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi a wannan makon an yi zaɓe a ƙasar Nijer

Zaɓe a NijerHoto: AP

Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afirka har da halin da ake ciki a ƙasar Nijer. A cikin sharhin da tayi game da wannan zaɓe jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung mai ra'ayin mazan-jiya cewa tayi:

"A ranar talatar da ta gabata shugaba Tanja na ƙasar Nijer ya tsayar da zaɓen sabuwar majalisar dokoki, bayan da ya rusa tsofuwar majalisar sakamakon ƙin yarda da tayi da shawararsa ta canza kundin tsarin mulkin ƙasar don yin ta zarce bayan mulki na tsawon shekaru goma. Ƙoƙarin da wakilan gamayyar tattalin arziƙin yammacin Afurka suka yi ƙarkashin jagorancin shugaban Liberiya Johnson-Sirleaf da tsofon shugaban Nijeriya Abdussalam Abubakar, don canza salon tunanin shugaban na Nijer bai cimma nasara ba. A dai halin da ake ciki yanzu Ƙungiyar Tarayyar Turai tayi gargaɗin cewar wannan zaɓen zai yi mummunan tasiri akan taimakon da take ba wa ƙasar, inda shugaba Sarkozy na Faransa yayi Allah Waddai da matakin na Tanja da cewar babbar barazana ce ga makomar demoƙraɗiya."

Shugaba Tandja na NijerHoto: AP

Ita ma jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi akan wannan ci gaba tana mai cewar:

"Dukkan abubuwan dake faruwa ka iya kaiwa ga taɓarɓarewar al'amura da rashin kwanciyar hankali. Hakan ya sanya gamayyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afurka ta tura wakilanta zuwa Nijer don ta su shawo kan shugabanta yayi sara tare da duban bakin gatarinsa. Amma kasancewar manzancin nasu bai yi nasara ba, a yanzun ba shakka ƙungiyar tarayyar Afurka zata shawarta akan tsauraran matakai na takunkumin da za a iya ƙaƙaba wa ƙasar ta yammacin Afirka."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau leƙa wa tayi ƙasar Somaliya don ba da rahoto akan wani sabon ci gaba mai ban mamaki a ƙasar inda ƙungiyar Al-Shabab mai iƙirarin kishin addinin musulunci ke farautar mata masu sa rigar nono don bulalesu. Jaridar ta ce:

Mayaƙan Al-Shabab a SomaliyaHoto: AP

"Dalilin da 'yan Al-Shabab suka bayar a game da wannan mataki nasu shi ne wai rigar nono na daga cikin hanyoyi na ɓata da Al-Ƙur'ani ke batu kansu. A saboda haka duk matar da suka kama ta da rigar nono za a yi mata bulala a ƙwace rigar nonon sannan ita kanta ta kakkaɓe rigar domin tabbatar da haramcinta a bainar jama'a."

A wani abin da ake gani tamkar kyakkyawan ci gaba bisa manufa, gwamnatin Amirka na shirin shiga tattaunawa da gwamnatin Sudan dangane da rikicin Darfur da kuma na kudancin ƙasar. Jaridar Der Tagesspiegel ce tayi nuni da haka ta kuma ƙara da cewar:

"Mawuyacin hali na rikicin da ake fama da shi a kudancin Sudan shi ne musabbabin wannan sabuwar alƙiblar siyasa da Amirka ta fuskanta. Domin kuwa a halin yanzu haka akwai barazanar wargajewar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2005, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar shekara ashirin da yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da miliyan ɗaya da rabi a kudancin Sudan. Sannan a yankin Darfur kuma tuni yaƙin basasar yankin ya canza ya ɗauki wani sabon salo na yaƙe-yaƙen gungun 'yan ta kife dake cin karensu ba babbaka a yankin."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu