1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen cike gurbi a ƙasar Libanon

August 5, 2007
A kasar Libanon an fara kada kuri´a a zaben cike gurbi don maye gurbin ´yan siyasar Libanon da aka yiwa kisan gilla. Ana daukar sakamakon da za´a samu daga wata mazaba daya da ta kasance hannun tsohon ministan masana´antu Pierre Gemayel, a matsayin zakaran gwajin dafin na goyon baya daga kiristocin kasar ta Libanon wadanda kawunan suke rarrabe. Ana gudanar da zaben a cikin tsauraran matakan tsaro don hana tursasawa da arangama tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna. Gwamnatin FM Fuad Siniora mai samun daurin gindin kasashen yamma ta kira zaben ba tare da amincewar shugaban kasa ba. ´Yan majalisar dokokin biyu da ake takara kan kujerunsu ´yan adawa da Syria ne kuma suna daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon gwagwarmayar rike madafun iko a kasar.