1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen magaddan gari a Brazil

October 7, 2012

Al'ummar kasar Brazil na ci gaba da ka'ɗa ƙuri'ar zaɓen magaddan gari cikin lumana.

Brazil's President Dilma Rousseff delivers a speech as Fernando Haddad, Sao Paulo mayoral candidate of the Workers Party, right, smiles during a campaign rally in Sao Paulo, Brazil, Monday, Oct. 1, 2012. The first round of Mayoral elections are scheduled for Oct. 7, and the second round on Oct. 28, 2012. (Foto:Andre Penner/AP/dapd).
Hoto: AP

Sama da mutane milyan 139 na 'yan ƙasar Brazil ne ke ka'ɗa ƙuri'unsu domin zaɓen wakilai da magaddan gari da ƙananan hukumomi kimanin dubu 5 da 568 da ke ƙasar. An buɗe runfunan zaɓen ne da misalin ƙarfe takwas na safe yayinda za a rufesu kuwa da misalin ƙarfe biyar na yamma. A ƙalla 'yan takara dubu 450 ne daga jam'iyyun siyasa 20 ke zawarcin kujeru dubu 1,500. Wannan zaben dai na a matsayin wani matakin farko kafin zaben shugaban ƙasar da za a yi a shekara ta 2014.

Mawallafi : Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh