Zaɓen shugaban ƙasa, a ƙasar Togo
March 3, 2010Talla
Ƙasar Togo wanda ta kasance tsohuwar renon ƙasar Jamus, ta ɗau shekaru da yawa tana ƙarƙashin mulkin kama karya, a ƙarƙashin jagorancin marigayi Gnassingbe Eyadema, har sai bayan da ya rasu. Inda daga nan aka naɗa ɗansa domin ya ga je shi. An wata mummunar zanga zanga a rikishin bayan zaɓen shekaru biyar da suka gabata, kuma an hallaka ɗaruruwan mutane. A bisa waɗannan dalai ya sa ake hasashen samun wani ruɗani a zaɓen wannan karon. Muddin dai Faure yace sai ya zarce ko ta halin ƙaƙa. Wannan hayaniya ce a tsakiyar kasuwar birnin Lome, wato babban birnin ƙasar ta Togo. Mata na ɗauke da kayan talla, akwai ƙananan shaguna, da kuma sauran masu saida kaya a tebura, wasu kuwa ƙarƙashin runfuna, inda ake sayar da kayan miya da sauransu. Ko da mai babur sai ya yi da gumin goshi kafin ya samu sukunin wucewa, domin yawan turereniya. Mai mota dai ba zai ma goda bin tsakiyar kasuwar ba. Don haka birnin Lome ya dogara kacokan da masu achaɓa irinsu Thomas Nate. wanda yace Babu aikin yi anan, makaranta na kasa yi, na fara gwadawa ko kasuwa za ta yu. Na fara da wani ɗan ƙaramin kayan tebur, amma lamarin ba daɗi, don haka yanzu sheka guda kenan da na fara sana'ar yin achaba" Kamar yadda lamarin yake ga Thomas, haka aksarin 'yan ƙasar ke fama, cikin shekaru dayawa. Sanadiyar hakan kuwa bai tsaya ga ƙarancin tattalin arzikin ƙasar ba, a'a harma da irin salon mulkin kama karya na tsohon shugaba Gnassingbe Eyadema, wanda ya ɗauki shekaru kusan arba'in yana mulkin ƙasar. Har sai a shekara ta 2005 da kwanan sa suka ƙare. Bayan mutuwar tasa, da aka so a naɗa ɗansa Faure, mutanen ƙasar sunyi zanga zanagar cewa anyi maguɗin zaɓe, kuma an hallaka masu zanga zanga fiye da 1000. Yanzu dai Farue yana son a sake zaɓen sa karo na biyu, to ko hakan zai kawo sauyi. Injiniya Kadjo Lare wani ɗan ƙasar ne da ya yi karatu a nan Jamus. Kuma yana mai cewa Idan zaka bashi maki bisa ayyukan da ya yi, to sai nace wani bala'ine mulkin sa a yanzu. Ka son ba za ma a tambayi masu zaɓe ra'ayinsu ba. Ƙuri'ar masu zaɓe bata kare buƙatunsu" Akwai dai mutane shidda dake takara da shugaba mai ci, ciki kuwa har mace guda. To amma idan akwai ɗaya daga cikinsu wanda zai samu nasara, to shine Jean-Pierre Fabre To ko yaya 'yan adawa suke kallon zaɓen?. Babu wanda zai je zaɓe, zaɓen da tuni an riga da an tattara sakamakon sa. A fili take jam'iya mai ci za ta faɗi zaɓen, amma ita za'a sanar da cewa ta lashe zaɓen. mu kuma ba za mu amince da haka ba, wannan shine tashin hankalin Tarayyar Turai dai ta koma ga baiwa ƙasar Togo tallafi bayan da dakatar da shi, biyo bayan tarzumar siyasa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace za su taimakane kawai, idan ana aiwatar da tsarin dimokraɗiyya, batun da shugaba Faure, yaci su ya sanya agaba, kuma ya ɗau alƙawarin baza'a zubar da jine ba a zaɓen. Bazan kariya ba, ko ma dami ya kasance a sakamakon zaɓen, kai ko da wani haɗari na tashin hankali ya biyo zaɓen Su ma dai 'yan ƙasar sun bayyana fatar su ga shugaban kamar haka "Shugaban ƙasa ya taimaka mana ga samun aiki saboda ba a samu aiki, ina fatan zai gina mana asibiti I ta kuwa wannan tace Abinda muke jira a gare shi, shi shugaban ƙasan, ya kammala ayyukan da ya sa a gaba, wanda za su sa birnin Lome ya yi kyau, ƙasar Togo ta yi daɗi Indan ana maganar ci gaba, dole sai ƙasa ta kasance ta na da hanyoyi na kwalta a koi´na Idan ba'a samu fitowar masu kaɗa ƙuri'a da yawa ba, to wani labarine mai daɗi ga shugaba mai ci. Don haka sai kawai ya yi iya murɗiyar da yakeso, daga nan sai a fara batun sauya kunɗin tsarin mulkin ƙasar. Ma wallafa:Alexande Göbel/ Usman Shehu Usman Edita: Ahmad Tijjani Lawal
Talla