Zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru
October 9, 2011
Rahotani daga ƙasar Kamaru sun ce an kamalla zaɓen shugaban kasa. Sai dai wanda suka ganewa idonsu yadda zaɓen ya wakana, sun ce babu tsari a ciki, sannan mutane ba su yi tururuwa a trufunan zaɓen ba.
A biranen Yaounde da Douala an ɗauki lokaci mai yawa kamin fara zaɓen.
`Yan takarar jam´iyun adawa sun zargi jam´iyar RDPC mai mulki tare da hadin gwiwa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ELECAM domin tafka maguɗi.
Masu adawar sun yi korafin cewar a mazabu da dama, babu katocin zaɓe illa na dan takara RDPC Paul Biya.
A jimilce runfunan zaɓe dubu 24 ne ya cancanta mutane kimanin miliyan bakwai su kada kuri´a daga jerin ´yan takara 23, wanda suka hada da shugaba mai ci yanzu Paul Biya ɗan shekaru 78 a duniya,wanda kuma ke kan karagar mulkin ƙasar Kamaru tun 1982, wato shekaru 29 kenan da suka gabata.
A ƙasar Kamaru, sabanin sauran kasashen Afrika, Hukumar zabe ta ELECAM ba ta izinin bayyana sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ƙasa , wannan yauni ya rataya akan kotun ƙoli. Kotun na da kwanaki 15 domin bayana wannan sakamako
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal