1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Masar

May 23, 2012

Yan takara guda 13 zasu fafata a zaɓen da shi ne karo na farko da ake gudanarwa bayan faduwar gwamnatin Hosni Moubarek

An Egyptian woman casts her vote inside a polling station in Cairo May 23, 2012. Egyptians vote on Wednesday for the first time to pick their president in a wide open election that pits Islamists against men who served under deposed leader Hosni Mubarak . REUTERS/Suhaib Salem (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Al'umma a ƙassar Masar na kaɗa ƙuria'a a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko; a karon farkon a ƙarƙashin tsarin jam'iyyun siyasa barkatai , tun bayan faɗuwar gwamnatin mulkin kama karya ta Hosni Moubarek a cikin watanni 15 da suka gabata.

Kimani mutane miliyion 50 ake sa ran zasu tantance tsakanin yan takara 13 wanda zasu tsaya a zaɓen,wanda ake kyautata zaton cewa Amr Moussa tsohon minista kana tsohon sakataran ƙungiyar ƙasashen larabawa,da kuma Abdoul Fatoh tsohon menba a cikin jam'iyar yan uwa musulmi suna iya samin nasara.To sai dai masu aiko da rahotannin sun ce jama'a da dama waɗanda ke nuna adawa da majalisar ƙolli ta mulki sojin ƙasar za su ƙauracewa zaɓen, kuma Samiha na da ga cikin masu irin wannan ra'ayi.''ta ce ina adawa da wanga zaɓe da sojoji suka shirya,ta ce kuma ban ga abinda zai sa na kaɗa kuria'a ba a zaben da sojojin zasu yi mirɗiya su baiwa wanda suke so mulki.

Mawallafi : Hassane Abdourahamane
Edita : Halima Balaraba Abbas