1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasar Masar zagaye na biyu

June 16, 2012

A kasar Masar an shiga zaɓen fid da gwani tsakanin Ahmed Shafik , tsohon jam'in gwamnatin Mubarak da Mohammed Mursi, na ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi.

Islamic presidential candidate Mohamed Mursi cast his vote in a polling station in Al-Sharqya, 60 km (37 miles) northeast of Cairo, May 23, 2012. Egyptians queued patiently to vote on Wednesday, eager to pick their leader for the first time in a national history dating to the pharaohs, with Islamists and secular-minded rivals who served under deposed President Hosni Mubarak heading the field. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

A wannan Asabar a ƙasar Masar aka fara zaɓen shugaba kasa zagaye na biyu tsakanin Ahmed Shafik, tsohon jami'in gwamnatin hamɓarraren shugaba Husni Mubarak da Mohammed Mursi, ɗan takarar ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi. Su dai waɗannan 'yan takara biyu sun gaza samun kuri'un da za su kai su ga darewa karagar mulki a zaɓen zagayen farko da ya gudana a watan Mayu. A ranakun Asabar da Lahadi ne dai za a gudanar da wannan zaɓe wanda wasu 'yan sa'o'i ƙalilan gabanin fara shi babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya yi kira ga al'umar kasar da su kada kuri'unsu cikin limana domin kauce wa kara tsunduma kasar a cikin rudamin siyasa.

A ranar Alhamis da ta gabata ba zato ba tsammani, kotun tsarin mulkin ƙasar ta rusa majalisar dokoki da aka girka watannin huɗu da suka shuɗe, abin da ya sa ake dasa ayar tambaya game da ko shin a shirye gwamnatin sojin ƙasar take ta mika ragamar mulki ga gwamnatin farar hula a karshen watan Yuni kamar yadda aka shirya. Wannan shawara da kotun da tsayar ta ta da hankalin ƙasa da ƙasa matuka ainun.

Mawalllafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal