1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Siriya ya ci karo da harin bama-bamai

May 7, 2012

'Yan adawar Siriya da suka ƙauracewa zaɓen 'yan majalisar dokokin da jam'iyu da yawa suka shiga, sun ce dodorido ne kawai.

epa03203966 Syrians walk past electoral banners and posters for the coming parliamentary elections at a street in Damascus, Syria, 02 May 2012. Syrian Parliamentary elections are scheduled for 07 May 2012. EPA/YOUSSEF BADAWI
Hoto: picture-alliance/dpa

Fashewar bama-bamai da faɗace faɗace a sassa daban daban na ƙasar Siriya suka mamaye zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar da magoya bayan gwamnati suka yi a ranar Litinin. Magoya bayan 'yan adawa sun ƙaurace wa zaɓen da suka kwatanta shi da cewa dodorido ne kawai. Masu boren ƙin jinin gwamnatin shugaban Siriyar Bashar Al-Assad a wasu wurare a Daraa da kuma yankunan Ƙurdawa sun yi kira da a gudanar da yajin aiki na gama gari. Masu sa ido a zaɓen sun ce ba a samu kwararar mutane zuwa rumfunan zaɓe ba. Sai dai ma'aikatar cikin gida a birnin Damaskus ta ce mutane da yawa suka fita kaɗa ƙuri'a. A wani labarin kuma masu fafatuka sun ce dakarun gwamnati sun kashe mutane da yawa a lardunan Hassaka, Deir as-Saur, Homs da kuma Damaskus. A Daraa da Hama da wasu wurare an samu fashewar bama-bamai da tashe tashen hankula.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu