Zaɓen 'yan majalisa na gaba da wa'adi a Girka a Afrilu
February 13, 2012Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Girka ta bayyana aniyarta ta gudanar da zaɓen 'yan majalisa na gaba da wa'adi a watan Afrilu mai zuwa idan Allah Ya yarda. Wannan matakin na Athens ya zo ne bayan da gwamnatin Papademos ta ɗibar wa kanta wa'adin wata guda da rabi domin aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu da majalisar dokoki ta amince da su. A watan oktoba mai zuwa ne dai ya kamata wa'adin mulkli na gwamnatin ta rikon kwarya karkashin Lucas Papademos ya zo karshe.
A daren lahadi zuwa litinin ne majalisar Girka ta amince da matakin tsimin kudi domin samun tallafin ceto karo na biyu daga ƙungiyar Tarayyar Turai da kuma Asusun bada lamuni na duniya. Sai dai kuma 'yan kasar ta girka sun shafe kwanaki suna zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu da matakan tsuke bakin aljuhu da gwamnati ta dauka. Kafafen watsa labaran ƙasar sun nunar da cewa kimanin mutane 120 ne suka ji raunuka lokacin zanga-zangar a birnin Athnes, yayin da masu zanga-zangar suka lalata gine gine da dama, tare da kwasar ganima a wasu shagunan.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal