Zaben 'yan majalisun Dokoki a kasar Habasha
May 24, 2015Talla
Sai dai abin kawai da ba'a sani ba, shi ne girman nasarar da gamayyar jam'iyyun da ke mulki tun daga shekara ta 1991 a ƙasar za su yi a wannan zaɓe, wanda kuma zai ba da damar sake mayar da Firaministan ƙasar Hailemariam Desalegn ga wani sabon wa'adin mulki.
Akalla dai 'yan ƙasar ta Habasha milian 36,8 ne za su zaɓi 'yan majalisun dokokin ƙasar da na jihohi a kalla 547 a zaɓen da ke a matsayin na farko tun bayan rasuwar shugaban ƙasar na wancan lokaci Meles Zenawi, wanda ya rasu sakamakon rashin lafiya a shekara ta 2012 bayan da ya shafe shekaru 20 a kan karagar mulkin ƙasar.