1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen ' yan majalisun dokoki a ƙasar Spain

November 20, 2011

Ana hasashen cewar jam'iyar masu ra'ayin riƙau za ta samu nasara a zaɓen domin kawo sauyi ga ƙasar da ke fama da matsalar tattalin arziki

Jose Luis Rodriguez Zapatero, fraministan Spain da mai ɗakin sa sun zo kaɗa ƙuria'a a runfar zaɓenHoto: AP

Kimani mutane miliyion 36 ake sa ran zasu kaɗa kuria'a a zaɓen yan majalisun dokoki na kafin wa'adi da ke gudana a ƙasar Spain.zaɓen wanda a ƙarƙashin sa za a sake zaɓen sabbin menbobin majalisar wakilai da na dattawa, na zaman jarabawa ga gwamnatin yan gurguzu ta Luis Rodrigez Zapatero wacce ta yi ƙaurin suna dangane da yadda ta kasa magance matsalar tattalin arziki da ta yiwa kƙasar katutu.

Wanda al ummar ƙasar galibi matasa da ke fama da rashin aikin yi ,ke zargi gwamnatin wajan gaza yin wani yunƙuri na rage yawan masu zaman kashe wando, da aka ƙiesta cewa zai iya kai kashi 21 cikin dari ,wata yar jaridar dake a birnin Madrid ta shaida yadda zaɓen ke gudana ''ta ce babu wani zumuɗi da jama'a suke da shi na fitowa da hima wajan kaɗa kuria'a ,ga zaɓen da aka riga aka yi hasashen cewar jam'iyar masu ra'ayin riƙau za ta samu nasara domin kawo ƙarshen mulki shekaru bakwai na jamiyar yan socialiste.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu