1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓukan gama gari a Sudan

April 10, 2010

Za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da zaɓukan na shugaban ƙasa, majalisar tarayya, jihohi da kuma gwamnoni

Zaɓe a Sudan

Bari mu fara da ƙasar Sudan inda a wannan Lahadin ake gudanar da zaɓen gama gari. A wani rahoto da ta rubuta jaridar Rheinische Merkur ta rawaito matasan ƙasar ta Sudan na cewa sun ƙuduri aniyar ganin shugaba Omar al-Bashir bai lashe wannan zaɓe ba domin a cewarsu abin ya kai musu iya wuya. To sai dai bisa yadda al´amura ke tafiya a Sudan, jaridar ta ce matasan waɗanda suka kafa wata ƙungiya mai suna Girifna ba za su yi wani kataɓus ba musamman ganin yadda hukumomin ƙasar ke tursasa musu. Hakazalika bisa la'akari da janyewa daga zaɓen da wasu manyan jam´iyun adawa suka yi, hakan zai bawa shugaba Al-Bashir cikakkiyar damar lashe zaɓe cikin ruwan sanyi.

Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob ZumaHoto: AP

Ita kuwa jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali ne kan Afirka Ta Kudu tana mai nuni da hukuncin kotu da ya haramtawa Julius Malema shugaban ɓangaren matasa na jam´iyar ANC rera wata waƙa da aka yiwa taken Kill The Boer, saboda kalamai na nuna wariya da waƙar ta ƙunsa. Ta rawaito ƙungiyoyin farar hula na yin tir da waƙar wadda a da ta kasance wata waƙar jinjinawa masu fafatukar yaƙi da mulkin wariyar launin fata wadda aka fara rera ta a shekarar 1993.

Har yanzu dai muna a ƙasar ta Afirka ta Kudu, inda a wani rahoto mai taken Afirka ta Kudu tana nuna alhini game da kisan gillan da aka yiwa Eugene Terreblanche, jaridar Neues Deutschland ta fara ne da cewa ko da a lokacin zaman kwanciyar hankali ne kisan Terreblanche zai ɗauki hankalin duniya baki ɗaya musamman kasancewarsa jagoran masu tsattsauran ra´ayi a wannan ƙasa da taɓa zama ƙarƙashin mulkin nuna wariyar launin fata. Duk da cewa dukkan 'yan siyasar ƙasar sun yi tir da kisan tare da yin kira da a kwantar da hankali amma magoya bayansa kashedi suka yiwa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da masu sha´awar wasan daga ko-ina cikin duniya cewa suna shirin zuwa wata ƙasa ta masu kisa, suna danganta kisan da aka yi shugaban na su da wani lamari da ya zama ruwan dare a Afirka Ta Kudu wanda kuma ka iya faruwa a lokacin wasan cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya.

Dirk Niebel da Guido Westerwelle a Pretoria, Afirka Ta KuduHoto: picture-alliance/dpa

Buɗe sabon babi a Afirka inji jaridar Frankfurter Rundschau a sharhin da ta rubuta game da ziyarar haɗin guiwa da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da takwaranasa ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa Dirk Niebel ke yi a wasu ƙasashen Afirka. Ta ce ziyarar da ministocin ke yi a ƙasashen Tanzaniya, Afirka Ta Kudu da kuma Jibuti za ta taka rawa wajen ɗinke ɓarakar dake tsakanin ma´aikatun guda biyu. Tuni dai masharhanta suka yi maraba da matakin ministan raya ƙasashe masu tasowa na bawa Afirka fifiko, domin wannan nahiya ta na sahun baya-baya a dangane da muradun raya ƙasashe masu tasowa na Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da a hannu ɗaya nahiyar ke ba da kyakkyawar damar zuba jari ga kamfanonin Jamus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi