Za a ba da tallafin corona a Amirka
December 22, 2020Tallafin zai lakume kimanin dala biliyan 900. A daren jiya Litinin aka cimma wannan matsaya bayan da aka dade ana kai ruwa rana a bukatun samar da kudadden tallafi na murmurewa daga radadin corona. Ana sa ran shugaban kasar Donald Trump zai sanya hannun nan da 'yan kwanaki masu zuwa kafin a soma aiwatar da aikin.
Za a yi amfani da wadannan kudadden wajen taimaka wa kamfanoni da masana'antu da kuma wadanda suka rasa aiyukansu. Amirka ce a sahun gaba daga cikin kasashen duniya da ta tafka asarar rayuka da dukiya a sanadiyar corona, mutum sama da miliyan goma sha takwas cutar ta kama wasu fiye da dubu dari uku suka mutu.
A daya bangaren zababben Shugaban kasar Joe Biden ya karbi allurar rigakafin cutar inda ya kara tabbatar ma 'yan kasa cewa babu wani abin fargaba a game da rigakafin.