Za a bawa sojin Iraki da na Kurdawa horo
December 8, 2014Talla
Kwamadan sojin Amirka da ke jagorantar kawance da ke yaki da IS Lt. Janar James Terry ya ce nan ba da jimawa bane dukannin shirye-shiryen da ake za su kammala da nufin ganin sojin na raki da Kurdawa sun samu cikakken horon da suke bukata.
Iraki dai da Siriya da ma wani bangare na Turkiyya na daga cikin wuraren da yanzu haka suka fi fuskantar baraza ta 'yan IS wanda ke rajin girka daular Musulunci kuma yanzu haka ake fafatawa da su a garin nan na Kobani da ke kan iyakar Siriya da Turkiyya.