Za a cigaba da zabe a wasu sassan Najeriya a yau
March 29, 2015An bude rumfunan zabe akalla 300 a fadin Najeriya don cigaba da kada kuri'u sakamakon gaza samun damar yi da aka yi jiya saboda matsaloli daban-daban.
Hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC ta ce ta yi hakan ne don baiwa al'ummar kasar damar kada kuri'arsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayyar ba tare da an tauye musu hakkinsu ba kamar yadda ya ke kunshe cikin dokokin zaben kasar.
Tun da misalin karfe goma na safiyar yau ne aka fara tantance mutane kana jami'an INEC din suka ce da karfe biyu na rana ne za fara kada kuri'a a wadannan mazabu 300 da ke warwatse a sassa daban-daban na Najeriya. A wuraren da aka samu yin zaben kuwa a jiya, jami'an hukumar da wakilai na jam'iyyu na cigaba da tattara sakamakon zaben a shiyyoyi kafin daga bisani a mikawa ofishin hukumar da ke Abuja don sanarwa a hukumance.
Can a Abuja kuwa musamman ma dai cibiyar karbar sakamakon zaben, wakilinmu Ubale Musa ya ce jami'an hukumar zaben ta INEC ciki kuwa har da shugabansu Farfesa Attahiru Jega sun shirya tsaf don tinkarar aikin fara tattara sakamakon zaben a matakain tarayya.
Zaben dai na jiya ya gudana ba tare da an samu matsaloli na tashin hankali ba kamar yadda aka yi hasashe ko da dai wakilanmu sun shaida mana cewar 'yan bindiga sun hallaka mutane a Gombe kana an samu tashin bam a Enugu da kuma mastaloli na isar muhimman kayan aiki na zaben a jihar Rivers da ke yankin Niger Delta, batun da ya sanya ake ta kiraye-kirayen soke zabe a jihar.