1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Shugannin BRICS na taro a Afirka ta Kudu

Abdourahamane Hassane
August 22, 2023

An taron kolin kungiyar kasashen BRICS a Afirka ta Kudu tare da ajandar fadada kungiyar ta kasashe masu tasowa zuwa kasashe masu karfin tattalin arziki.

Hoto: JAMES OATWAY/REUTERS

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa mai masabkin baki zai gana da shugabannin kasashen Brazil da Indiya,da China da jagoran diplomasiya na Rasha Sergey Lavrov a Johannesburg. Tuni dai  shugaban Kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya isa birnin da shi da shugaban China Xi Jinping. A karkashin sammacin kame daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan laifukan yaki a Ukraine, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai shiga taron ne kawai ta hanyar bidiyo.Taron na BRICS karo na 15 na zuwa ne cikin rarrabuwar kawuna na kasashe sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.