Ghana ta samu tallafin rigakafi
February 24, 2021Talla
A karkashin tsarin nan na Majalisar Dinkin Duniya na tallafin alluran rigakafin Corona wato COVAX, Ghana ta zama kasa ta farko da ta fara karbar tallafin a fadin duniya.
Kimanin alluran na kamfanin harhada magunguna na AstraZeneca 600,000 ne kasar ta karba a wannan laraba.
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hakan na zama wani babban cigaba da aka samu na yaki da annobar kuma ba za a kawo karshen ta ba har sai an game ko ina da rigakafin.
Ghana kamar sauran kasashen duniya da suka fara bayar da rigakafin, za a fara ne da mutane mafiya hadarin kamuwa da cutar kamar tsofaffi da masu rashin lafiya ta musamman da kuma ma'aikatan kiwon lafiya.