Cibiyar rigakafin Corona ta farko zata fara aiki a Jamus
November 24, 2020Talla
Biyo bayan samun maganin cutar COVID-19 da aka yi, gwamnatin Jamus zata bude cibiyar rigakafin cutar Corona ta farko a kasar.
Ministan lafiya na kasar Jens Spahn shine ya tabbatar da hakan a wata tattaunawar da aka yi da shi. Ministan ya ce tuni ya bukaci gwamnatocin jihohin kasar dasu ware cibiyoyin da za a fara wannan aikin, kamin nan da tsakiyar watan Disamba mai kamawa.
Tuni dai kasar ta Jamus ta tanadi alluran rugakafin sama da miliyan 300, haka ma lamarin ya ke a mafi yawancin kasashen kungiyar Tarayyar Turai wadanda suka amince da ingancin maganin.
Adadin wadanda suka kamu da cutar ta Corona a Jamus din yanzu haka ya kai 942,687 inda 14,361 suka rigamu gidan gaskiya sanadiyar cutar.