1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Za a yanke wa mai lalata da matasa hukunci a Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou
January 9, 2026

A tarayyar Jamus, wani matashi mai lalata da matasa ya shiga hannun hukuma, kuma a wannan Jumma'ar zai urfana gaban alkali don yanke masa hukunci.

Deutschland | Polizeieinsatz
Hoto: Marijan Murat/dpa/picture alliance

Wata kotu a nan Jamus ta fara shari'ar wani dan asalin Jamus mai tsatso da Iran mai shekaru 21 a wannan Juma'a a birnin Hamburg, bisa tuhumarsa da yaudarar yara matasa ta yanar gizo don cin zarafinsu da kuma lalata.

Matashin mai suna Shahriar J. zai bayyana agaban alkali ne da misalin 12 na rana a asirce a gaban wata kotu ta musamman da ke kula da kananan yara.

Ko baya ga aikata lalata da kananan yara, kotu na zargin matashin da laifuka fiye da 200 da ya aikata kan mutane akalla 30, yawancinsu yara a tsakanin watan Janairu na shekarar 2021 zuwa Satumba na shekarar 2023.

An kama matashin ne tun a shekarar 2021, sai dai kuma bisa kasancewarsa yana da shekaru 16 a lokacin aka jinkirta sharii'ar har zuwa wannan shekara kuma a wannan rana.