1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amirka za ta fitar da sunan Sudan daga bakin littafi

Ramatu Garba Baba
September 23, 2020

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta shirya fitar da sunan Sudan daga cikin jerin sunayen kasashen da ake zargi da laifin taimakawa ayyukan ta'addanci a duniya, don ita ma ta ci moriyar da sauran kasashen duniya ke ci.

Sudans neuer Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Makonni kalilan kafin a gudanar da babban zaben kasar Amirka, kasar ta dauko hanyar gyara dangantakarta da kasar Sudan. Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ce ta shirya da ta fitar da sunan Sudan daga cikin jerin sunayen kasashen da ake zargi da laifin  taimakawa ayyukan ta'addanci a duniya don ita ma ta ci moriyar da sauran kasashen duniya ke ci.

Sakataren harkokin wajen Amirka, Mike Pompeo ya ce matakin na a matsayin nuna goyon baya ne ga sabuwar gwamnatin Khartoum da ta yi nasarar kawar da shugaban da ke mata mulkin kama karya, lamarin da ya janyo aka sanya ma kasar tarin takunkumi. Firai Minista Abdallah Hamdok ya nuna sha'awar dinke baraka a tsakanin kasar Sudan da Amirka tun bayan da ya dare mulki.

Dangantaka dai ta yi tsami a tsakanin Amirka da Sudan bayan da shugaban kasa a wancan lokaci Oumar al-Bashir ya bai wa jagoran Kungiyar al-Qaeda mai da'awar jihadi mafaka, daga bisani an sami mayakan na al-Qaeda da laifin hannu a kai hare-hare a ofisoshin jakadancin Amirka da ke Kenya da Tanzaniya inda aka sami asarar rayuka sama da dari biyu. Amirka ta soma shirin biyan diya ga iyalai da wadanda harin ya rutsa da su inji Sakatare Pompeo.