Za a gina sansani mafi girma a Bangladesh
October 18, 2017Talla
Gwamnatin ta dauki matakin ne don samun damar magance kwararar 'yan gudun hijrar Rohingya na kasar Myanmar da ke tserewa rikice-rikicen kabilanci a kasarsu, ana ganin in har an yi nasarar gina sansanin zai kasance sansani na 'yan gudun hijra mafi girma a duniya. Yanzu haka 'yan gudun hijrar Rohingya fiye da dubu dari biyar ne suke samun mafaka a Bangladesh yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsaloli na daukar dawainiyarsu.
Hukumar 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana da 'yan gudun hijra fiye da miliyan sittin da biyar da ake tsugune da su a sansanonin na 'yan gudun hijra daban daban a duniya.