Za a girka gwamnatin haɗin gwiwa a Jamus
November 27, 2013Talla
Shugabannin na jam'yyun siyasar guda uku wato Angela Merkel ta (CDU), da Sigmar Gabriel ta (SPD) dakuma Horst Seehofer na (CSU),a ƙarshe sun ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu a kan yarjejeniyar inda suka amince da batun albashi mafi ƙanƙanta na Euro takwas a awa guda da maganar kuɗaɗen fanso da kuma ritaya.
An kwashe wattannin biyu tun bayan zaɓen 'yan majalisun dokokin da ya gudana a cikin watan Satumba da ya wuce ana ta yi shawarwari a kan wannan batu ba tare da samun nasara ba sai a wannan jiƙon. Jam'iyyun siyasar dai sun kai ga saka hannu a kan yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin gwiwar a nan gaba a ƙarshen wani taron da ya gudana inda wakilan suka kaɗa ƙuri'a akai a cikin daren jiya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu