Ana zaben raba gardama kan kudin tsarin mulki a Guinea
September 21, 2025
Al'ummar kasar Guinea Conakry za su kada kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, shekaru hudu bayan da sojoji suka yi juyin mulki. Sabon kundin tsarin kasar zai ta bayar da damar gudanar da zabe, sai dai kuma za ta ba shugaban majalisar mulkin sojin kasar, Janar Mamady Doumbouya damar tsaya wa takarar shugaban kasar. Jam'iyyun adawar kasar sun ce za su kaurace wa kada kuri'ar zaben na wannan Lahadin.
Karin bayani: Guinea Conakry: Shakku kan alkawarin zabe
'Yan adawar dai sun ce zaben raba gardama wani shiri ne da aka tsara domin sojoji su ci gaba da rike madafun ikon kasar. Sabon kundin tsarin mulkin zai soke ikrarin da Janar Doumbouya a lokacin kwace ikon kasar da tsinin bindiga, inda ya ce babu wani dan majalisar mulkinsa da zai shiga zaben shugaban kasa. Kimanin mutane miliyan takwas ne daga cikin al'ummar kasar miliyan 14 da rabi suka yi rijistar zaben da ake sa ran bude rumfuna a gaba kadan. An kuma sa ran baza jami'an tsaro dubu 45 domin tabbatar da tsaro.