1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Za a je zagaye na biyu a zaɓen ƙasa na Nijar

January 2, 2021

Bayan gaza samun wanda ya samu kason da ake bukata kafin zama shugaban kasa, 'yan takara biyu masu neman kujerar shugabanci a Nijar za su sake komawa fagen fama.

Niger Wahlzentrale Niamey
Hoto: DW/A. Adamou

Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyya mai Mulki a Jamhuriyar Nijar, Malam Bazoum Mohamed, zai fuskanci tsohon shugaban kasa Mahamne Ousmane a zagaye na biyu na zabe.

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar na zaben ranar Lahadin da ta gabata ne ya nunar da hakan a wannan Asabar.

A zagaye na farko na zaben dai, Malam Bazoum Mohamed ya sami kashi 39.33% na kuri’un da aka kada, yayin da Mahamane Ousmane ke da 17%

Dama dai ana bukatar dan takara ya sami akalla 51% ne kafin a bayyana shi  a matsayin wanda ya lashe zabe.