1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Fargabar barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya

Abdourahamane Hassane
August 9, 2024

Isra'ila ta amince a ci gaba da tattaunawa a ranar 15 ga watan Augusta da nufin sassantawa da Hamas da kuma sako mutanen da ake yin garkuwa da su

Hoto: Moritz Frankenberg/dpa/picture alliance

 Hakan ya biyo bayan shiga tsakani na Amurka, da Masar da Qatar  wadanda  suka yi  gargadin cewar lokaci na kurewa. Wannan shawara na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a yankin zirin Gaza,inda akalla mutane 18 suka mutu  a hare-haren da Isra'ila ta kai kan makarantun boko biyu a cewar Hamas,Yanzu haka dai ana nuna damuwa da kuma fargaba a kan barkewar yaki a yankin na Gabas ta Tsakiyya baki daya a kan wannan rikici wanda ya hada da Iran da   Libanon