1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutanen da suka mutu a azumin ganin yesu ya kai 70

Abdul-raheem Hassan
April 24, 2023

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon umarnin wani limanin coci na hana su cin abinci ya haura 70 a Kenya. Gwamnati ta sha alwashin daukar matakin kan mumunar akidar.

Kenya
Hoto: Stringer/REUTERS

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya sha alwashin murkushe wani abin da ya ce ba za a minta da shi ba na wani limamin coci da ya kashe mutane da yunwa da ziummar hada su da Almasihu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da 'yan sandan suka tabbatar da tono karin wasu garwakin da adadinsu ya kai 73 a ranar Litini, hukumomi sun ce ana cigaba da binciken karin wasu gawarwaki a wani dajin da ke kusa da garin Malindi da ke gabar teku.

A shekarar 2017, 'yan sanda sun kama paston mai suna Nthenge bisa zargin yada tsatsauran akida bayan hana kai yara makaranta, yana mai cewa Littafi Mai Tsarki bai amince da ilimin boko ba.