Za a saki dan jaridar da aka kama a Masar
June 16, 2014Babban mai gabatar da kara ba Masar ya bada umarnin sakin Abdullah Al-Shamy, dan jaridar nan na Al-Jazeera da ya shafe kwanaki 130 ya na yajin cin abinci don nuna rashin amincewa da tsare shin da ake yi ba tare da shari'a ba. Wata sanarwa da aka fidda kan sakin na Al-Shamy ta ce an yanke shawarar sallamarsa ne da wasu mutane 13 saboda rashin koshin lafiya da suke fama da ita.
A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai aka tsare dan jaridar da takwarorinsa bisa zargin kasancewarsu 'yan kungiyar nan ta 'yan Uwa Musulmi ta Shugaba Muhammad Morsi da ma taimaka musu wajen yi wa gwamnatin kasar zagon kasa, zargin da Al-Sahmy din da abokan aikinsa suka musanta.
Kasashen duniya da dama kafofin watsa labarai a duniya sun yi sukar lamirin gwamnatin Masar na tsare 'yan jaridar da ma gaza gabatar da wasunsu gaban kuliya domin yi mu shari'a, lamarin da ake gani tamkar tauye hakkin 'yancin fadin albarkacin baki ne.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman