Za a sami karancin agaji a duniya
February 19, 2019Talla
A wani kiyasin da ta yi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kudaden da kungiyoyin za su bukata don ci gaba da samar da agajin a Yemen da wasu sassa na duniya, za su kai sama da dalar Amirka biliyan hudu.
Jagoran hukumar agajin na Duniya Mark Lowcock, ya shaida wa taron kwamitin sulhu cewar batun cimma bukatun jin kai a kasashen duniyar, shi ne babban kalubalen da ke gabansu a yanzu.
A ranar 26 ga wannan watan na Fabrairu ne dai ake sa ran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin na Duniya, Antonio Guterres ya shirya wani taro a birnin Geneva na kasar Switzerland kan wannan bukata.