Duniya za ta sake fuskantar karancin abinci
July 17, 2023Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sha yin Allah wadai da cikas da kasarsa ke fuskanta a kokarin fitar da kayayyakin abinci da taki zamani zuwa ketare, wanda ya kamata ya yi dai-dai da hatsin da Ukraine ke fitarwa. Sannan ya bayyana cewar kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba game da alkawarin da aka yi na isar da hatsi ga kasashe masu karamin karfi musamman a nahiyar Afirka. Wannan sanarwar ta zo ne 'yan sa'o'i kalilan kafiin cikar wa'adin yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine ta tekun Black Sea wacce aka cimma a watan Yulin 2022 a kasar Turkiyya. Wannan rashin sabunta yarjejeniyar hatsin na zama martanin Moscow ga harin da Ukraine ta kai kan gadar Crimea wanda ake amfani da ita wajen kai kayan yaki ga sojojin Rasha da suka mamaye kasar. Sojojin ruwa na kasar Ukraine sun tabbatar da amfani da jirage marasa matuka wajen kai wannan harin, wanda ya salwantar da rayukan fararen hula biyu tare da raunata 'yarsu. Sai dai majalisar dattijan Rasha da kanta ce ta nemi gwamnati Moscow ta mayar da martani ta hanyar kai hari
An yi tsammanin Putin zai tsawaita yarjejeniyar
Yarjejeniyar ta ba wa Ukraine damar fitar da kusan ton miliyan 33 na hatsi, duk da rikicin da take fama da shi. Sai dai kasancewar an taba sabunta ta sau biyu, ya sa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi yakinin cewar Mista Putin zai sake ba da damar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa tekun Black Sea. "Na yi imani abokina na Rasha Vladimir Putin yana son wannan aiki na jin kai ya ci gaba. A halin yanzu, ministan harkokin wajena zai gana da takwaransa na Rasha, kuma zan gana da Mista Putin nan ba da jimawa ba, bayan na dawo daga balagoru a yankin Gabas ta Tsakiya. Idan muka gana da shi a watan Agusta, za mu sami damar tattaunawa kan dukkan wadannan batutuwa, kuma za mu yi nazari kan yadda za mu yi aikin share fagen jigilar kayayyakin abinci da taki na Rasha."
Turkiyya na kokarin shiga tsakani domin samar da cimmakar
Dama dai Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya sun shafe karshen mako suna jagorantar tattaunawar karshe don shawo kan Rasha ta tsawaita yarjejeniyar hatsi da aka kulla a watan Yulin 2022, amma hakarsu ta kasa cimma ruwa. Sai dai bayanan da aka samu daga cibiyar JCC da ke kula da yarjejeniyar ta Istanbul, Chaina da Turkiyya ne suka fi cin gajiyar yarjejeniyar ta hatsi da kuma wasu kasashe masu karfin tattalin arziki. Jamus da ke zama daya dga cikinsu ta yi kira ga Rasha da ta bayar da damar tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine zuwa ketare, saboda matakin da ta dauaka zai yi mummunan tasiri a kasashe mafi talauci a duniya. Sannan a lokacin da yake gudanar da taron maneman labarai kan wannan batu a birnin Berlin, Christian Hoffmann, kakakin gwamnatin Jamus ya yi fatan ganin wannan yarjejeniya ta hatsi ta tashi daga na kayyadadden lokaci. "Kuma muna fatan ganin cewa nan gaba wadannan yarjejeniyoyin hatsi ba za a iya amince da su na wucin gadi ko na wani dan lokaci kadan ba, amma muna fatan ganin zai yiwu nan gaba kadan a mayar da wa'adin dogon zango na fitar da hatsi da taki daga Ukraine." Albarkacin wannan yarjejeniya fitar da hatsin Ukraine, hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta bayar da tallafin jin kai ga wasu kasashe goma sha biyu da ke cikin mawuyacin hali kamar Afghanistan da Sudan da Yemen.