Za a soma shari'ar kisan Sankara
October 13, 2017Thomas Sankara ya rasu ne a shekarar 1987 a wani juyin mulki da hambararren shugaba Blaise Campaore ya jagoranta. Sai dai ba a taba dago batun shari'arsa ba a tsawon shekarun da Blaise Compaore ya shafe yana mulki duk da cewa tun bayan mutuwarsa an yi ta samun zanga zanga daga magoya bayansa da ma iyalansa da suka nemi a gudanar da bincike don gano da kuma hukunta duk wadanda keda hannun a mutuwar jagoran sauyi a kasar.
A shekarar 2015 aka tono gawar da ake kyauta zato na tsohon shugaban ne da zummar gudanar da bincike na tabbatar da cewa gawar ta sa ce da kuma musababbin mutuwarsa.Thomas Sankara ya kasance mutumin da ya jagoranci fafutukar 'yantar da kasar ta Burkina Faso ta hanyar bijiro da sabbin tsare tsare sai dai kafin ya cimma burinsa , Blaise Campaore ya hambarrar da shi a shekarar 1987.