1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron COP27 ya amince a taimaka wa kasashe matalauta

Ramatu Garba Baba
November 20, 2022

An karkare taron COP27 tare da cimma matsaya na ganin an taimaka wa kasashen da suka tafka asara a sakamakon matsalar sauyin yanayi da kudi.

COP27 Klima-Konferenz | Sameh Shoukry
Hoto: Peter Dejong/AP/picture alliance

Mahalartar taron sauyin yanayi sun cimma matsaya na samar da kudadde don tallafa wa kasashen da suka fi tafka asarar a sakamakon matsalar da sauyin yanayin ta haifar musu, an kai matakin a taron da aka fi sani da COP 27 da ya gudana a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh da ke kasar Masar.

Wannan batu na rage wa kasashe matalauta radadin asarar, ya sa an tsawaita taron da aka saba yi na mako biyu da kwana guda. A yayin da ake kallon hakan a matsayin ci gaba, su kuwa masu rajin kare muhalli na ganin akwai sauran rina a kaba, ganin taron bai kai ga cimma matsaya a yarjejeniyar rage yawan hayakin da ke gurbata iska da manyan kasashen duniya suka fi fitarwa ba, wanda kuma shi ne tushen matsalar da ke haifar da matsalolin na sauyin yanayi.