Za a tallafa wa Sudan wajen fita kangin bashi
May 17, 2021Talla
A taron za a duba yiyyuwar ceto kasar daga basussukan da suka yi mata katutu da kuma yadda za a janyo masu saka hannun jari.
Taron na yau na zuwa ne kwana guda gabanin wani taron da Faransar ta tattara shuwagabanni da ma'aikatan diplomasiya na nahiyar Afirka ta yadda Faransar za ta taimaka wa kasashen wajen murmurewa daga masassarar tatalin arzikin da kasashen nahiyar suka shiga bayan tu'annatin da annobar Corona ta yi masu.
Faransar da ba ta wuce wani dan yanki ba a daya daga cikin kasashen nahiyar ta Afirka, ta bayar da tabbacin halartar manyan shugabannin kasashen nahiyar da suka hada da Abdel Fattah al-Sisi na Masar da Paul Kagame na Ruwanda da shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya wanda tuni ya yada zango a kasar ta Faransa.