Jami'an Rasha da UKraine za su tattauna
February 28, 2022Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince da tattaunawar yayin da sojojin Putin da tankokin yaki suke kara kutsawa cikin kasarsa
A waje guda Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojinsa masu kula da makamin nukiliya su kasance cikin shirin ko ta kwana.
Vladimir Putin ya kara kambama tashin hankali tsakanin yankin gabashi da yammaci bayan da ya umarci sojoji masu kula da makamin nukiliya su zauna cikin shiri.
Putin ya danganta matakin da abin da ya kira kakkausar sanarwar da NATO ta yi da kuma tsauraran takunkumin tattalin arziki da aka sanyawa kasarsa.
Wannan dai ya sanya fargabar cewa rikicin na Ukraine na iya rikidewa zuwa yaki da makamin kare dangi walau da ganga ko kuma da kuskure.
Amirka ta bukaci Putin ya sassauta kausasan kalamai masu hadari da yake yi na barazana da makamin Nukiliya.