Za a tuhumi mataimakin shugaban kasar Kenya
June 3, 2013Talla
Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto zai gurfana a gaban Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC, bisa tuhumar sa da hannu cikin rikicin bayan zaben shekara ta 2007 da aka yi a kasar.
Sashen tuhuma na kotun ta ICC, ya sanar da cewa zai fara sauraron shari'ar Ruto, a ranar 10 ga watan Satumba mai zuwa, domin baiwa bangaren masu kare wanda ake kara isasshen lokaci da za su shirya.
Ruto, mai kimanin shekaru 46 a duniya, na fuskantar tuhumomi uku da suka danganci aikata manyan laifuka kan dan Adam, bisa rawar da ya taka a rikicin bayan zaben kasar na shekara ta 2007 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1000.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu