Za a yi taro babban taro kan COVID-19
November 5, 2020![Symbolbild Corona PCR Test](https://static.dw.com/image/55093673_800.webp)
Talla
A dazu ne babba zauren Majalisar Dinkin Duniya din ya amince da yin wannan taro wanda zai hada kan shugabannin kasashen duniya da nufin tattauna matakan da za a dauka wajen dakile yaduwar cutar.
Gabannin wannan zama da ake sa ran yinsa tsakanin 3 da 4 ga watan Disamba dai, kasashen duniya ciki har da Jamus da Faransa da Ingila sun tsaurara matakan yaki da cutar inda Ingila ta sanya dokar kulle a fadin kasar baki daya.