Za a yi taro kan Siriya a Astana
January 17, 2017![Russland Sergej Lawrow in Moskau](https://static.dw.com/image/36953902_800.webp)
Talla
Babban jami'n diflomasiya na kasar Rasha Serguei Lavrov ya ce daya daga cikin manufofin da ake da su a taron da kasashen Rasha da Turkiya da Iran za su yi a ranar 23 ga wannan wata a Astana shi ne na kara tabbatar da shirin tsagaita wuta a Siriya.Kasashen Rashar da Iran na goyon bayan gwamnatin shugaba Bashar Al Assad yayin da Turkiyar ke goyon bayan 'yan tawayen Siriyar.