Za a yi wa Chadi da Afirka ta Tsakiya tsakani
June 2, 2021![Flagge der Afrikanischen Union](https://static.dw.com/image/57656672_800.webp)
Talla
Chadi dai ta zargi dakarun sojin Afirka ta Tsakiya da kisan sojojinta, lamarin da ya sanya ministoci uku na kasar ta Afirka ta Takiya yin tattaki ya zuwan Chadin a jiya Talata domin bin ba'asin abin da ya faru.
Da ma dai akwai wata jikakka tun a shekara ta 2013, bayan da Chadin ta shiga cikin kasashen kungiyar AU a lokacin da Afirka ta tsakiya ta shiga yakin basasa. Batun na Chadin na cikin abubuwan da kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta ECCAS za su tattauna a babban taronsu da za fara a gobe.